Matthew 18

1Daidai wannan lokacin, almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, ‘’Wanene mafi girma a mulkin sama?‘’ 2Sai Yesu ya kira karamin yaro gunsa, ya sa shi a tsakaninsu, 3ya ce, ‘’Hakika ina gaya maku, idan baku juya kun zama kamar kananan yara ba, babu yadda zaku shiga mulkin sama.

4Saboda haka, duk wanda ya kaskantar da kansa kamar karamin yaron nan, shi ne mafi girma a mulkin sama. 5Duk wanda ya karbi karamin yaro a suna na, ya karbe ni. 6Amma duk wanda ya sa daya daga cikin ‘yan yaran nan da suka gaskanta da ni zunubi, gwamma a rataya dutsen nika a wuyansa a jefa shi cikin zurfin teku.

7Kaiton duniya saboda lokacin tuntube! Lallai ne wadannan lokuta su zo, amma kaiton mutumin da ta wurinsa ne wadannan lokutan za su zo! 8Idan hannunka ko kafarka ce za ta sa ka tuntube, ka yanke ta, ka yar daga gare ka. Zai fi maka kyau ka shiga rai da nakasa ko gurguntaka, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta tare da hannayenka ko kafafunka.

9Idan idonka zai sa ka tuntube, ka kwakule shi, ka yar. Zai fi maka kyau ka shiga rai da ido daya, da a jefa ka cikin madawwamiyar wuta da idanu biyu.

10Ku kula fa kada ku rena kananan nan. Domin koyaushe a sama, mala’ikunsu na duban fuskar Ubana da ke sama. 11[Dan Mutum ya zo ya ceci abinda ya bata].

12Menene tunaninku? Idan mutum na da tumaki dari, sa’annan daya ta bata, ashe ba zai bar tassa’in da tara a gefen tudu ya tafi neman wadda ta bata ba? 13In ya same ta, hakika ina gaya maku, farin cikinsa na samun dayan nan da ta bace, zai fi na tassa’in da taran nan da basu bata ba. 14Hakanan fa, ba nufin Ubanku dake sama ba ne da ya daga cikin wadannan kananan ya hallaka.

15Idan dan’uwanka yayi maka laifi, fada masa tsakaninku, kai da shi kadai. Idan ya saurare ka, ka maido da dan’uwanka kenan. 16Amma in ya ki ya saurare ka, ka je da ‘yan’uwa biyu ko uku su zama shaidu, don ta wurin shaidu biyu ko uku ake tabbatar da kowacce kalma.

17In kuma ya ki ya saurare su, ka kai lamarin ga ikklisiya. Idan ya ki ya saurari ikklisiya, ka maishe shi ba‘al’umme da mai karbar haraji.

18Hakika ina gaya maku, duk abin da kuka daure a duniya, a daure yake a sama. Abin da kuka kwance kuma, a kwance yake a sama. 19Kuma ina gaya maku, idan mutum ku biyu zaku yarda akan duk abin da zaku roka, Ubana wanda ke a sama zai yi maku shi. 20Wurin da mutum biyu ko uku suka taru a cikin sunana, zan kasance tare da su.‘’

21Bitrus ya zo ya ce wa Yesu, ‘’Ubangiji, sau nawa ne dan’uwana zai yi mani laifi in gafarta masa? Har sai ya kai sau bakwai?‘’ 22Yesu ya amsa ya ce masa, ‘’Ban gaya maka sau bakwai ba, amma bakwai din ma har sau saba’in.

23Saboda haka, za a kwatanta mulkin sama da wani sarki da yake so ya lisafta dukiyarsa dake a hannun barorinsa. 24Da ya fara yin haka, sai aka kawo masa daya daga cikin barorinsa da yake binsa talanti dubu goma. 25Amma tunda ba shi da abin biya, ubangidansa ya bada umurni a sayar da shi, tare da matarsa da ‘ya’yansa da duk mallakarsa, domin a biya.

26Sai baran ya fadi kasa, ya rusuna a gaban ubangidansa ya ce, “Maigida, kayi mani hakuri, zan biya duk abin da na karba.” 27Don haka ubangidansa yayi juyayi, sai ya ce, ya yafe bashin, a saki baran.

28Amma bayan an saki wannan baran, ya je ya sami wani baran kamar sa da yake bi bashin dinari dari. Ya cafke shi, ya shake shi a wuya, ya ce, ‘Ka biya bashin da nake bin ka.’ 29Amma dan’uwansa bara ya roke shi ya ce, kayi mani hakuri, zan biya ka duk abinda na karba.’

30Amma baran nan na farko ya ki. A maimakon haka, ya sa aka jefa dan’uwansa bara a kurkuku sai ya biya bashin nan. 31Da sauran barori suka ga abin da ya faru, suka damu kwarai. Sai suka je suka fada wa ubangidansu yadda abin ya faru duka.

32Sai ubangidansa ya kirawo shi, ya ce masa, ‘’Kai mugun bawa, na gafarta maka bashin nan duka, domin ka roke ni. 33Ashe, bai kamata kaima ka nuna jinkai ga dan’uwanka bara kamar yadda na nuna maka jinkai ba?’

34Ubangidansa yayi fushi, ya danka shi ga masu azabtarwa, har sai ya gama biyan dukan bashin da ake binsa. Hakanan Ubana dake a sama zai yi maku, idan kowannenku bai gafarta wa dan’uwansa daga zuciya ba.‘’

35

Copyright information for HauULB